Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ministar tsaron Faransa ce, Florence Parly, ta bayyana hakan, a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar.
Ta ce dama Faransa ta gargadi Mali da cewa, kasancewar ‘yan daba na Kamfanin Wagner a Mali, ba zai tafi daidai ba da kasancewar sojojinta da na wasu kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa ba.
Cacar baki tsakanin Mali da Faransa ta dada kamari ne tun bayan jawabin da firaministan Mali, ya yi a zauren babban taron MDD, inda ya bayyana cewa Faransa ta juya wa Mali baya.
Saidai Faransar ta bakin ministar tsaron kasar ta ce, yauta ne ma a yi tsamannin cewa Faransa za ta fice daga Mali.
A jawabin da ya yi a zauren MDD, firaministan mali. Chogel Maiga, ya ce kasarsa bata ji dadi ba akan yadda kawayenta da Faransa da kuma MDD, basu sanar da ita ba akan matakin, janye dakarun tawagar Barkhane.
Malin, ta koka da yadda a cewarta al’amuran tsaro basu daidaita ba duk da kasancewar dakarun ketare a kasar inda ‘yan kasar ke ci gaba da fuskantar barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Hakan ne sanya Mali, ta yi gaban kanta, ta dauki batun tsaro da mahimmanci, bayan da dakarun Barkhane sukayi watsi da ita, a cewar firaministan na Mali.
Saidai Mali ba ta ambato zargin cewa tana shirin hadin guiwa da sojojin haya na kasar Rasha ba, wanda ya tada kura tsakaninta da faransa.
342/